LABARUN KARSHEN WATA

DAGA TASKAR MURYAR TALAKA


Tare da: Jibril Almustapha Gusau

***Gobara ta tashi a babbar tashar rarraba hasken wutar lantarki ta jihar Zamfara dake shiyyar Samaru, Gusau. Lamarin dai ya auku ne a yammacin ranar Lahadin nan da ta gabata. Kawo yanzu dai hukumar samar da hasken wutar lantarki ta KEDCO dake da alhakin rarraba wutar lantarki a jihar Zamfara bata bayar da wata sanarwar dalilin faruwar lamarin ba a hukumance. Talakawa a fadin jihar Zamfara suna cikin fargabar rashin samun hasken wutar lantarki da wasu sassan jihar zasu iya fuskanta.

***Kungiyar Muryar Talaka ta shirya tsab, domin gudanar da zaben sabbin shuwagabannin ta na kasa da zai gudana a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Kungiyar, ta nada babban kwamitin tsare-tsaren wannan zabe mai membobi biyar da suka hada da:
1- Aktibis Muhammad Lawal Gusau a matsayin Shugaba, da
2- Murtala Muhammad Bello Gusau, a matsayin Ma'aji; da
3- Alhaji Kwamared Umar Gidado Gummi a matsayin jami'in hulda da jama'a na daya, da
4- Abdulmalik Sa'idu Mai Biredi a matsayin jami'in hulda da jama'ah na biyu. Sai kuma
5- Hafizu Balarabe Gusau a matsayin Sakataren Kwamitin.

A ranar 4 ga watan Agusta ne dai ake sa ran gudanar da taron masu ruwa-da-tsaki na kungiyar, wanda ake sa ran zai samu karbar bakuncin Babban Ministan Matasa da Wasanni, Barista Solomon Dalung, da kuma mai taimaka wa Shugaban Kasa aka kafafen sada zumunta, wato Malam Bashir Ahmad. A yayin da Mai Daraja Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman zai kasance mai masaukin baki.

***Mukaddashin Shugaban kasar nan Farfesa Yemi Osinbajo ya kawo ziyarar aiki ta wuni daya a jihar Zamfara. Rahotanni sun nuna cewa, Osinbajo ya bude ayyukan raya kasa daban-daban da gwamnatin jihar Zamfara tayi karkashin jagorancin Gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar.

***Majalisar Dattijai da ta Wakilai sun aminta da dabtarin kudurin rage shekarun cancantar yin takara a fadin kasar nan wanda aka yiwa lakabi da #NotTooYoungToRun bill, a turance. Majalisun dai sun nuna goyon bayan su ne ta hanyar samun amincewar sama da kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar.

A halin yanzu dai ana jiran majalisun dokokin jihohi su zauna suyi bitar wannan dabtarin kuduri. Wanda ake sa ran samun amincewar akalla majalisun jihohi 24 cikin 36 da muke dasu a fadin kasar nan, kafin a gabatar dashi gaban shugaban kasa domin rattaba hannu.


***Gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari Abubakar ya aminta da nada Alhaji Muhammad Bawa a matsayin sabon Sarkin Tsafe. Kafin nadin nasa dai, shi ne yake rike da sarautar Yariman Tsafe. Rahotanni sun nuna cewa, tuni sabon 'yandoton Tsafen ya karbi takardar kama aiki daga hannun Mai Daraja gwamnan jihar Zamfara. Nadin nasa ya biyo bayan rasuwar mai martaba 'yandoto Habibu Aliyu, wanda Allah yayi wa rasuwa a makon jiya.

Comments