Mun Shirya Tsab, Domin Gudanar Zaben Muryar Talaka Na Kasa
Daga: Muhammad Lawal Gusau A wata sanarwa da kwamitin tsare-tsare na gudanar da babban zaben kungiyar Muryar Talaka ta kasa ya fitar, ta hannun jami'in hulda da jama'a na kwamitin, Kwamred Umar Gidado Gummi, inda ya bayyana cewa: "Yanzu haka dukkanin shirye-shirye sun kammala kan wani sabon tarihi da Gusau zata kafa. Bayan share lokutta shugabannin wannan kungiya a matakin kasa da uwayenta keyi na tattauna wannan taron da muka gayyata. Nayi karbar wayoyi da dama kan wannan shiri kuma na bayyana wa kowa da kowa cewa, mun shirya tsab, daga gobe alhamis duk wanda ya iso Gusau masaukinsa na nan daram. Mun ringa mun tanadar da shi. Gidado ya kara da cewa: "Bisa wannan muke bada umurni ga dukkanin sauran wakillanmu da zasu halarto wannan taro dasu daura tuta, mai taken "National Congress Gusau". Bayan haka kowa ya tabbatar da ya dauko katin shaidar sa na zama halastaccen dan kungiya. Kafin ya kamo hanyar zuwa gurin wannan taro." Kwamred Gummi ya...